Thursday 20 October 2011

Gyada: Abar Alfaharin mu.

Ban yi Hangen cewar abubuwa za su tabarbare kamar haka ba, lalacewar da idan kai ba dan wani bane karatu zai zo ya gagari dalibi a kasarsa ta haihuwa. Halin ko in kula da son kai da wadanda ke rike da matakan iko ke yi wa ilimi, ya kai wani munzali da babu alamar tausayin talaka.
Sama’ila da Abubakar ‘yan uwan juna ne, iyalai sama da mutum goma sha takwas (18) mahaifinsu ya rasu ya bari shekara biyu da suka wuce. A yanzu, suna karkashin kulawar mahaifiyarsu tare da taimakon kakanninsu.
“Ni shekarata goma sha bakwai (17), shi kuma yana bi na da sha shida (16)”- a cewar Sama’ila babban cikinsu.
Wadannan yara, a duk sati suna baro kauyensu wanda yake da tazarar 40km tsakaninsa da Kano, sau biyu domin shigowa yin talla. Me suke sayarwa? Gyada!
“Daga Garko muke zuwa, mu kan taho daga karfe takwas na safe mu koma gida karfe bakwai na yamma”. Wannan hanya ta su kuwa, ta yi kaurin suna wajen manyan hadduran mota sakamakon kasancewarta babbar hanya ta shigowa Kano daga wasu birane. Matsalolin wannan hanya ta Maiduguri da sauran gurare sun hada da: hannun dayan titin, gangancin masu manyan motoci, rashin iya tukin masu ababen hawa da ke bin hanyar da kuma karya dokar hanya wanda ba wani sabon abu bane ga mai bin manyan hanyoyi a kasarnan. A wannan yanayi, wadannan yara wadanda ya kamata a ce suna marantunsu domin daukar darasi, ke tangaliliya da rayuwarsu.
“Mu kan biya naira dari da ashirin (N120) kowanne mu a matsayin kudin mota duk lokacin da za mu taho. Mu kan dauko tallar gyadar dubu biyu(N2000) kowannemu, idan da kasuwa mu kan sayar da har ta dubu da dari biyar(N1500). Kowanne kulli naira hamsin (N50) mu ke sayarwa”. Shin a wanne yanayi suke gudanar da tallar? Waje daya suke zama ko kuwa yawo suke?
“Daga nan inda mota ta sauke mu, daga nan za mu fara tallarmu. Wasu lokatanma, tun daga cikin mota za mu fara cin kasuwarmu. Babu wani takamaiman waje da za mu ce muna zama, duk inda ta kama tafiya muke- kama daga bakin hanya, bakin shaguna, kasuwa, unguwanni kai ko’ina”.
Dubban yara kamar wadannan na nan na yawo kwararo-kwararo a cikin birnin Kano da kwaryarta, za mu iya cewa Sama’ila da Abubakar sun yi dace da samun sana’ar yi, wasu sa’anninsu da yawa ba sana’ar sai shaye-shaye da zaman banza. Haka dai lamarin ke ci gaba da kasancewa a kullum, wanda kuma ba wani muhimmin kokarin gyara kan wannan annoba. Rayuwar  manyan gobe na cikin garari.....
“muna zuwa makarantar Islamiyya, amma akan hada mana da karatun boko. Dalibai a ajinmu guda dari da sittin  (160) ne.  Ina aji uku (3) shi kuma yana aji biyu (2)”.
Akwai son karatu sosai a wajen wadannan yara, amma yanayi da suka samu kansu ciki shi ya hana cikar burinsu. Wannan kuwa ba zai wuce nasaba da halin rashin babu ko talauci ba. Karajin da mahukunta ke yi na kokarin tabbatar da ilimi kyauta a saukake ga yara ya zamanto tatsuniya.
Duk dubban ko miliyoyin da gwamnati ta kance ta ‘ware kan ilimi’, hakar ba ta cimma ruwa ba. Makarantu na nan babu malaman kirki, ajujuwan babu rufi, ba kujerun zama balle wani cikakken tsari na tafiyar da bada ilimin kansa. A wasu guraben ma babu makarantun kwata-kwata, balle yaran su sami damar koyon.
A yanayi irin wannan, a iya cewa rayuwar da akwai ban tsoro a ciki. Ingattaciyar rayuwa ba ta samuwa cikin jahilci. Ya zama tilas a kawar da tallace-tallace a tsakanin yaranmu, a mayar da su makarantu, a ba su kyakkawan tarbiyya a kuma dora su kan tafarki wanda za su dogara da kansu idan sun girma. Wannan hakki ne da ya rataya akan kowa ba gwamnati kadai ba.
“Mu kanmu ba ma tunanin rayuwarmu za ta dore a talla, amma ba yadda za mu yi. Dole mu ci abinci, mu rayu mu kuma taimakawa mahaifiyarmu”. In ji Sama’ila.
Fata na kenan, haka zalika fatan duk wani mai tausayi da son ci gaba kenan. Zai fi kyau a ce yau tallar takardar shaidar ilimi ake yawo da ita kurfa-kurfa ba gyada ba. Burinsu a yanzu, su sami ilimi ko da na sanin dabarun yadda za a fitar da mai daga gyadar domin yin girki.